1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

EU ta damu da sabon matakin Isra'ila

July 19, 2018

Kungiyar Tarayyar Turai ta ce bata ji dadin sabon matakin da Isra'ila ta dauka kan 'yancin dan kasa ba.

Polen, Warschau: Proteste gegen Regierungsreformen
Hoto: Getty Images/W. Radwanski

Kungiyar Tarayyar Turai wato EU ta bayyana damuwa kan matakin da majalisar dokokin Isra'ila ta dauka na bayyana cewa Yahudawa ne kadai ke da cikakken 'yancin dan kasa.

A cewar kungiyar ta EU, matakin wata gagarumar matsala ce ga shirin samar da zaman lafiya tsakanin Isra'ila da kuma Falasdinu.

Da safiyar wannan Alhamis ne dai Isra'ilar ta amince da dokar, bayan shafe watanni ana ta tabka turanci a kanta.

Tuni dai larabawa marasa rinjaye suka soki matakin, suna mai bayyana shi da wariya karara.

Dokar ta kuma soke amfani da harshen larabci a matsayin harshe da ake amfani da shi a hukumance

Larabawa dai na matsayin kashi 20% na Isra'ilar mai yawan mutum miliyan tara.