EU na son Rasha ta rage harajin gas
September 7, 2022Talla
Shugabar Hukumar Tarayyar Turai Ursula von der Leyen ta bayyana wasu jerin matakai da za a bi wajen magance matsalar tashin gauron zabi da farashin makamashi ya yi, daga ciki har da kayyade farashin iskar gas din Rasha.
Jim kadan da fadin hakan, Shugaban Rasha Vladimir Putin ya mayar da martani, yana mai barazanar dakatar da samar wa kasashen Turan makamashin na gas, inda ya kira yunkurin da sunan wauta. Putin ya gargadi shugabanin kasashen na EU da su guji abin da zai kai ga haifar da tsadar makamashin a duniya.
Shugaban da ya kaddamar da yaki kan Ukraine sama da watannin shida da suka gabata, ya ce, zai ci gaba da yakar Ukraine har sai hakarsa ta cimma ruwa.