EU ta gaza amince da kakaba wa Rasha sabbin takunkumi
July 15, 2025
Ministocin harkokin wajen kungiyar Tarayyar Turai sun gaza amincewa da shirin kakabawa Rasha takunkumin tattalin arziki a karo na 18, a kan yakin da ake yi a Ukraine, bayan da Slovakia ta ci gaba hawa kujerar kin amincewarta.
Jami'ar kula da harkokin wajen EU Kaja Kalas, bayan taron ministoci a Brussels wanda yakin Ukraine ya kasance babban agenda, ta nuna rashin jin dadinta da rashin cimma yarjejeniyar.
Matakin da ake shirin dauka na ladabtarwa ya shafibangarorin kudi da makamashi na kasar Rasha, wanda ke a matsayin martani ga kin amincewa da shugaba Vladimir Putin yayi, na tsagaita bude wuta a Ukraine ba tare da wani sharadi ba.
Sai dai andakatar da takunkumin bayan da Firaministan Slovakia Robert Fico, a watan da ya gabata ya ayyana rashin amincewarsa da wannan kudiri, yana mai nuni da damuwar kasarsa akan bukatu na iskar gas.