1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

EU ta haramta lalata kayan sakawa

July 19, 2026

A wannan lahadin ne, dokar hana zubar da kayan sakawa da kuma takalman da shaguna ba su sayar ba ta fara aiki a tarayyar Turai.

 EU ta haramta lalata kayan sakawa
EU ta haramta lalata kayan sakawaHoto: Odelyn Joseph/AP Photo/picture alliance

A duk shekara ana lalata dubban tan na kayan sakawa a fadin kasashe 27 mambobin EU saboda sun lalace, ko kuma sun tsufa a shagunan ko kuma wadanda aka dawo da su bayan an siya a intanet.

Ana sa ran sabuwar dokar za ta shafi manyan dillalan kayan sawa, masu sayar da kayan sari. A karkashin dokar, an haramta wa manyan kamfanoni masu ma'aikata sama da 250 da kuma kudaden shigarsu na shekara-shekara da ya zarce euro miliyan 50, lalata kayayyakin da ba a sayar ba, kamar su tufafi, kayan kawa da takalma.

A yanzu ya zama wajibi kamfanoni su nemo hanyoyin sayar da kayan, ta hanyar bayar da rangwame da neman wasu kasuwanni da kuma bayar da su a matsayin gudummawar agaji.

Za a fadada dokar, wadda Brussels ta amince da ita tun fiye da shekaru biyu da suka gabata, ta shafi matsaikatan kamfanoni a shekarar 2030.