1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAsiya

EU ta haramtawa jami'an gwamnatin Iran shiga kasashenta

Abdulkarim Muhammad Abdulkarim
January 12, 2026

Daruruwan mutane suka mutu a Iran sanadiyyar zanga-zangar adawa da tsadar rayuwa da aka fara ranar 28 ga Disamban 2025.

Shugaban Iran Masoud Pezeshkian tare da shugaban tarayyar Turai António Costa, yayin tattaunawa da juna a birnin New York na Amurka
Shugaban Iran Masoud Pezeshkian tare da shugaban tarayyar Turai António Costa, yayin tattaunawa da juna a birnin New York na Amurka Hoto: Ilna.ir

Majalisar tarayyar Turai ta sanar da haramtawa jami'an diflomasiyyar Iran da ma na gwamnati shiga kasashenta, sakamakon zarginta da amfani da karfi fiye da kima a kan masu zanga-zangar adawa da tsadar rayuwa a kasar.

Shugabar majalisar Roberta Metsola, ta ce Turai ba za ta taba aminta da yadda gwamnatin Iran ke gallazawa al'ummarta ba, har ma da kashe wasunsu, kamar yadda ta wallafa a shafinta na sada zumunta na X ranar Litinin.

Karin bayani: Zanga-zangar Iran: Trump na tunanin daukar matakin soji

Daruruwan mutane ne suka rasa rayukansu a yayin wannan zanga-zanga, wadda aka fara a ranar 28 ga Disamban shekarar da ta gabata ta 2025.

Ko a ranar Lahadi sai da Roberta Metsola ta shawarci mahukuntan Iran su sauya salon yadda suke tunkarar masu boren, domin daina kashe su.

Tsallake zuwa bangare na gaba Bincika karin bayani