SiyasaTurai
EU ta jingine tattaunawa kan mafakar siyasa
September 20, 2023![](https://static.dw.com/image/66796806_800.webp)
Talla
Kasashen Turan sun gaza cimma matsaya ne kan wannan batu mai matukar sarkakiya, lamarin da ya kara jefa Jamus cikin tsaka mai wuya, wadda a watan Yulin da ya gabata ta nuna rashin amicewarta da matakin.
Jamus din dai ta nuna damuwarta kan yadda za a iya samun jan kafa wajen bai wa masu neman mafakar siyasar kulawar da ta kamata.
Wakilin Jamus a majalisar dokokin Turan Michael Claus ya bukaci a hanzarta komawa kan teburin tattaunawa don gaggauta cimma matsayar da ta dace a kan batun.