1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Taron EU kan bakin haure ya watse baram-baram

Gazali Abdou Tasawa
July 18, 2019

Taron ministocin cikin gida na kasashe mambobin Kungiyar Tarayyar Turai kan batun 'yan gudun hijira da ya gudana a ranar Laraba a birnin Helsinki na kasar Finland ya kawo karshe ba tare da cimma matsaya ba. 

Italien Lampedusa | Rettungsschiff Alex Hafeneinfahrt ohne Erlaubnis
Hoto: picture-alliance/AP Photo/Ansa/Elio Desiderio

Kasashen Faransa da Jamus ne dai suka kira wannan taro da nufin daukar matakin dakatar da haramcin da wasu kasashen Turan ke yi wa jiragen ruwa masu aikin ceto bakin haure a kan teku, a game da shiga tashoshin ruwan kasashensu domin sauke mutanen da suka ceto da kuma tattauna batun rarraba 'yan gudun hijirar a tsakanin kasashen na Turai. 

Sai dai ministan cikin gidan kasar Italiya Matteo Salvini ya yi tsayiwar gwamin jaki kan matsayin kasarsa na adawa da shigar jiragen ruwan masu aikin ceton bakin hauren akan teku a tashoshin ruwan kasar.