1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Jami'an Turai sun taya Birtaniya murna

Zainab Mohammed Abubakar
October 24, 2022

Charles Michel shugaban majalisar gudanarwar kungiyar Tarayyar Turai gami da Roberta Metsola shugaban majalisar dokokin Turai suka bada sanarwar taya Sunak murna.

UK Premierminister Rishi Sunak
Hoto: Jacob King/empics/picture alliance

Manyan jami'an kungiyar Tarayyar Turai biyu sun taya Rishi Sunak murna kan shirin zama sabon firaministan kasar Birtaniya na gaba bayan lashe kujerrar shugabancin jam'iyyar Conservative mai mulki tare da fata kan iya daidaita lamuran kasar.

Shi dai Rishi Sunak wanda zai zama sabon firaministan Birtaniya ya kasance tsohon ministan kudin kasar, kuma zai zama firaminista na biyar cikin shekaru shida da suka gabata, abin da ke nuna irin tsaka mai wuya na siyasa da aka shiga a kasar ta Birtaniya.