Iran na bitar shawarwarin EU
August 8, 2022![Österreich Burgenland | Treffen zu Iran Atomabkommen](https://static.dw.com/image/61268574_800.webp)
Talla
Iran ta ce tana sake bitar shawarwarin da aka tsayar don ceto yarjejeniyar ta nukiliya aka cimma a 2015 da kasahen yammacin duniya, bayan da kungiyar Tarayyar Turai ta gabatar da kundin karshe na tattaunawar ceto yarjejeniyar a ranar Litinin.
A ranar Alhamis ce kasashen Biritaniya da Chaina da Faransa da Jamus da Iran da Rasha da kuma Amirka suka sake komawa teburin tattaunawa a Vienna, watanni bayan dakatar da batun.