Kungiyar EU ta yi fatali da tsarin Birtaniya
September 21, 2018Talla
Masu iko daga EU sun yi watsi da tsare-tsaren Firaminista Theresa May ta Birtaniya kan batun da ya shafi tattalin arziki tsakanin bangarorin biyu idan an kammala da shirin ficewar Birtaniya daga Kungiyar EU.
A cewar May dai tsarin da ta zo da shi, shi ne mafita wajen kare huldar kasuwanci da kasashen na Turai idan kasar ta fita daga kawancensu na kasuwanci a kasuwar bai daya, da ma batun da ya shafi jami'an kwastam da hulda da yankin Ireland. Sai dai daga bangaren na shugabanni a Kungiyar EU sun nunar da cewa tsarin na May zai iya zama barazana ga kudirin kasuwar bai daya da suke da ita tsakanin kasashensu.