1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

EU ta yi watsi da sakamakon zaben Venezuela

August 1, 2024

Kungiyar Tarayyar Turai, EU ta ce ba za ta amince da Nicolas Maduro ba a matsayin wanda ya lashe zaben shugaban kasar Venezuela, har sai an kammala kirga zabe.

Babban jami'in diflomasiya na kungiyar Tarayyar Turai EU, Josep Borrell
Babban jami'in diflomasiya na kungiyar Tarayyar Turai EU, Josep BorrellHoto: Urs Flueeler/dpa/picture alliance

Babban jami'in diflomasiya na kungiyar Tarayyar Turai EU, Josep Borrell ya ce hukumar zaben Venezuela ta bayyana sakamakon ne bayan kirga kashi 80 cikin 100 na kuru'u.

Karin bayani: Venezuela: Shugaba Maduro ya lashe zabe karo uku

Ya kara da cewa, sakamakon zaben da bangaren adawa suka gabatar ya sha bambam da na hukumar. A ranar Larabar ne, shugaba Maduro ya sha alwashin cewa, bangaren adawa ba zai  taba mulkar kasar ba. Batun da ke ci gaba da jawo suka kan sahihancin zaben da haifar da zanga-zanga da ta bar baya da kura.

A kalla mutane 11 ne aka tabbatar da mutuwarsa sakamakon zanga-zangar kan zaben da ake zargin an tafka magudi.