Babban taron EU a gabanin yarjejeniyar Brexit
October 17, 2019Talla
Rahotanni sun ce tuni bangarorin da ke shiga tsakani kan batun ficewar Birtaniyar sun nuna cewa an samu muhimmin ci gaba a tattaunawar da ake, kana kuma hakan kan iya kai ga bangarorin biyu cimma wata yarjejeniya a gabanin ficewar Birtaniya daga EU.
Taron na kwanaki biyu da shugabannin za su gabatar dai na a matsayin na karshe ga Birtaniya, gabanin shirye-shiryen ballewar kasar daga kungiyar a ranar 31 ga wannan watan.
Ko baya ga batun na Brexit wata majiyar diflomasiya ta tabbatar da cewa, shugabannin za su kuma tattauna muhimman batutuwan da dama da suka shafi kungiyar, ciki har da bayyana matsaya guda kan batun luguden wutar da Turkiyya ke yi wa mayakan Kurdawa da ke kasar Siriya.