Sojojin EU za su ci gaba da zama a gabar tekun Libiya
March 17, 2021Talla
Kungiyar ta EU ta fidda wannan sanarwar ne a wannan rana ta Laraba, ta bakin wani babban jami'inta.
Jami'in ya ce a mako mai zuwa ne za a kai karshen wannan batu, wanda zai ba da damar ci gaba da girke dakarunsu har nan da karshen watan Maris din shekarar 2023.
Tun bayan kifar da gwamnatin shugaba Mu'ammar Ghaddafi makamai suka fara bazuwa daga kasar zuwa wasu kasashen Afirka da yanzu suke fama da matsalolin tsaro.
A baya babban sakataren Majalisar Dinkin Duniya Antonio Gutteres ya yi kira ga kasashen duniya da su yi hobbas wajen kawo karshen rikicin kasar ta Libiya ko a sami dakile bazuwar da makamai ke yi a ko ina.