EU za ta daina cinikin mai da Iran
June 26, 2012Ministocin harkokin waje na kasashen da ke da kujera a kungiyar Tarayyar Turai sun amince mambobin Eu 27 sun katse cinikin man fetur da kasar Iran. Wannan sabon mataki sun dauke shi da nufin ci gaba da matsa wa hukumomin Teheren lamba domin su yi watsi da shirin kera makakin kare dangi da ake zarginsu da yi a asirce. A Ranar lahadi daya ga watan juli mai kamawa ne dai wannan takunkumi zai fara aiki.
A baya dai fadar mulki ta Teheran ta yi barazanar katse tattaunawa da ta ke yi da manyan kasashen duniya game da shirinta na nukiliya idan aka kakaba mata wani sabon takunkumin karaya tattalin arziki. Kasashen yammacin duniya suna nuna shakku game da shirin inganta uranium da Iran ke yi, suna masu zarginta da amfani da wannan dama domin mallakar makamin nukiliya. sai dai Iran ta na ci gaba da wanke kanta inda ta ke cewa shirin nukiliyarta na inganta halin rayuwar talakawanta ne.
Mawallafi:Mouhamadou Awal
Edita: Usman shehu Usman