1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

EU za ta dau matsaya kan bukatar Ukraine

Abdul-raheem Hassan
May 9, 2022

Hukumar Tarayyar Turai za ta sanar da matsaya kan bukatar Ukraine na zama mamba a kungiyar, wannan dai wani muhimmin mataki ne da hukumar ta dauka gabannin matakin karshe na kasashe 27 a watan Yuni.

EU-Parlament - Ursula von der Leyen
Hoto: Jean-Francois Badias/AP Photo/picture alliance

A cikin sakon da ta wallafa a shafinta na twitter, shugabar hukumar kungiyar ta EU Ursula von der Leyen ta ce ta yi magana da shugaban kasar Ukraine Volodymyr Zelensky, kuma tana fatan samun amsoshin tambayoyin zama mambobin Ukraine.

A watan Afrilu, von der Leyen ta ziyarci Kyiv don nuna goyon baya ga Ukraine kuma ta amince cewa Brussels za ta yi la'akari da dadewar burin Ukraine na shiga kungiyar.

Wannan na zuwa ne a dai-dai lokacin da kasar Rasha ta yi bikin cika shekaru 77 kan nasarar yakin duniya na biyu a kan 'yan Nazi a kasar kasar Jamus. Amma kuma a jawabin da shugaban kasar Vladmir Putin ya yi, ya fi mayar da hankali ne a kan mamayar da kasarsa ke ci gaba da yi a Ukraine.