EU za ta hana shigar da makamai Libiya
January 20, 2020Talla
Kantoman da ke kula manofofin kasashen ketare na EU din Josep Borrell ne ya ambata hakan bayan kamamla zama da ya yi da ministocin kasashen ketare na kasashen da ke kungiyar kan rikicin na kasar ta Libiya.
Baya ga batun dakile shigar da makamai kasar ta Libiya, Borrell ya ce EU za ta yi bakin kokarinta wajen ganin an tabbatar da yarjejeniyar tsagaita wuta da aka cimma tsakanin bangarorin da ke kai ruwa rana a kasar.
Wannan dai na zuwa ne kwana guda bayan wani zama na musamman da aka yi a birnin Berlin na tarayyar Jamus kan rikicin Libiya din, wanda ya samu halartar shugabanin wasu kasashen duniya da kuma babban sakataren Majalisar Dinkin Duniya gami da shugaban kungiyar kasahen Afirka ta AU.