1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

EU za ta je Isra'ila kan sabbin hare-hare a Gaza

March 23, 2025

Babbar jami'ar diflomassiyar kungiyar Tarayyar Turai Kaja Kallas za ta ziyarci Isra'ila sannan ta kara sa yankin Falasdinawa a ranar Litinin domin gaggauta dawo da aiwatar da yarjejeniyar tsagaita wuta.

Hoto: sabel Infantes/Pool Photo/AP/picture alliance

Ofishin jami'ar ta Turai ya sanar da haka a wannan Lahadi, yana mai cewa a yayin ziyarar, Kallas, za ta tattauna rikicin Gaza, ta tunasar da bangarorin da abin ya shafa muhimmancin bude kofar shigar dakayan agaji a Zirin Gazada hanzarta dawo da aiwatar da yarjejeniyar sakin fursunonin siyasa da dakatar da kai hare-hare.

Jami'ar za ta tattauna da ministocin Isra'ila da na Falasdinu domin shawo kan sabon rikicin da ya sake kaurewa a makon nan bayan harin da Isra'ila ta kai.

MDD ta ce Zirin Gaza ya shiga cikin mawuyacin hali tun bayan sabbin hare-haren da Isra'ila ta dawo da su bayan makonni shida da aka kwashe ana aiki da tsagaita wuta.

Tsallake zuwa bangare na gaba Babban labarin DW

Babban labarin DW

Tsallake zuwa bangare na gaba Karin labarai daga DW