1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Turai za ta taimaka wa Nijar da magunguna

Abdul-raheem Hassan
October 19, 2023

Kungiyar Tarayyar Turai ta shirya kai wa Nijar tallafin magunguna masu mahimmanci, matakin na zuwa ne a daidai lokacin da kasar ke fama da takunkuman karya tattalin arziki a matsayin horo bayan juyin mulkin a watan Yuli.

Wasu 'yan kasar Nijar kenan ke karfafawa sojoji gwiwaHoto: AFP/Getty Images

Kasar Nijar na fama da matsi sakamakon janyewar da manyan kasashen duniya da ke tallafawa kasar ta fuskar tsaro da tattalin arziki, ita ma kungiyar raya tattalin arzikin kasashen yammacin Afirka ECOWAS ta sa kafar wando guda da sojojin da suka kifar da gwamnatin dimukuradiyya karkashin Shugaba Mohamed Bazoum. Sojojin sun zargin gwamnati da rashin dakile amyakan jihadi da suke hana zaman lafiya a kasar.

Kungiyar EU wacce ta dakatar da tallafin kudi ga sojin Nijar, za ta ce jirgin farko na magungunan ya riga ya sauka a birnin Niamey a ranar 8 ga watan Oktoba na shekarar 2023. Kungiyar ta kara da cewa kungiyoyin agaji da ke aiki a Nijar sun fuskanci matsalar hanyoyin samar da muhimman kayayyaki da zai rage wa al'ummar kasar radadin tsadar rayuwa na hauhawar farashin kaya.

Firayim Ministan Nijar Ali Mahaman Lamine Zeine ya da shirin tsuke bakin aljihu da zai ba da fifiko wajen kashe kudade kan harkokin tsaro da albashin jami'ai, inda gwamnatin ta kaddamar da asusun hadin kai don gudanar da ayyuka.