1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kungiyar Tarayyar Turai za ta tallafa wa Afirka

Ramatu Garba Baba
February 11, 2022

Wannan shi ne karon farko da Kungiyar Tarayyar Turai ke bijiro da shirin da zai taimaka wajen inganta rayuwar al'ummar nahiyar Afirka ta hanyar zuba jari.

 Ursula von der Leyen
Hoto: Virginia Mayo/AP/picture alliance

A gabanin soma taron koli a tsakanin Turai da nahiyar Afirka, Kungiyar Tarayyar Turan ta baiyana wani sabon shirin tallafawa kasashen Afirka. Shugabar kungiyar Ursula von der Leyen ce, ta jagoranci kaddamar da shirin da ake fatan zai taimaka a inganta rayuwar al'umma nahiyar ta hanyar zuba jari na kimanin yuro biliyan dari da hamsin a Afirka. Babu dai karin bayani da ta yi na yadda za a samar da wadannan makuddan kudaden.

Shirin kungiyar wanda shi ne irinsa na farko, na da zummar bunkasa harkokin kasuwanci a tsakanin nahiyoyin biyu ta hanyar jan hankulan manyan kasashen duniya don zuba jarinsu a kasashen na Afirka musanman kasashen da ke fuskantar karancin kudi.

Yanzu haka babbar jami'ar na ziyarar aiki a birnin Dakar na kasar Senegal a gabanin babban taron koli na Kungiyar Tarayyar Turan da takwararta ta AU da za a soma daga ranar 17 zuwa 18 na wannan watan Febrairun wannan shekarar ta 2022.