1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaJamhuriyar Dimukuradiyyar Kwango

Shugaba Tshisekedi zai sha rantsuwar tazarcewa kan mulki

Abdoulaye Mamane Amadou
January 20, 2024

A Jamhuriyar Dimukuradiyyar Kwango shugaba Félix Tshisekedi zai sha rantsuwar kama aiki, bayan kotu ta tabbatar da nasarar lashe zaben shugaban kasar.

Shugaba Felix Tshisekedi na Jamhuriyar Dimukuradiyyar Kwango
Shugaba Felix Tshisekedi na Jamhuriyar Dimukuradiyyar KwangoHoto: AFP

Za a rantsar da Shugaba Félix Tshisekedi na Jamhuriyar Dimukuradiyyar Kwango, bayan da kotun kolin kasar ta tabbatar da shi a matsayin wanda ya lashe zaben shugaban kasa da aka gudanar mai cike da cece-kuce.

Ana dakon halartar manyan baki daga ciki da wajen Kwangon a bikin, da ke zama irinsa na biyu a tarihin rayuwar Félix Tshisekedi mai shekaru 60 a duniya. Masu hamayya da suka hada da  Moïse Katumbi da Martin Fayulu da suka sha kaye a zaben, na ci gaba da fatali da sakamakon zaben, inda suka yi kira ga magoya bayansu da su fito zanga-zanga.