1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Faɗa na ƙara yin ƙamari a Libiya

March 13, 2011

Dakarun gwamnatin Libiya na kan hanyar kaiwa ga cibiyar 'yan tawaye a Benghazi

Hoto: dapd

Dakarun da ke goyon bayan kanal Gaddafi na ƙoƙarin ƙara dannawa yankin gabashin Libiya a birnin Benghazi inda nan ne cibiyar 'yan tawayen. Bayan da suka samu ƙarin nasara akan wasu garuruwa da suke cikin hannu yan adawar, inda suka yi amfanin da jiragen yaƙi na sama da na ruwa da kuma manyan tankokin yaƙi domin tilasawa baraden 'yan tawayyen ja da baya.

Masu aiko da rahotanin sun ce sun ga 'yan tawayen a garin Brega cibiyar samar da man fetur suna arcewa cikin motoci zuwa ƙuryar yankin gabashin bayan da dakarun gwamnatin suka karɓe birnin. Har ya zuwa yanzu ƙasashen duniya sun kasa cimma wata matsaya bayan taron ƙungiyar NATO da ƙungiyar Tarayya Turai akan saka takunkumi hanna shawagin jiragen yaƙin Libiya a sararin samaniyar ƙasar. Yayin da a gobe litinin aka shirya ƙungiyar ƙasashe masu ƙarfin tattalin arzikin masana'antu G8 za ta gudanar da wani zaman taro na musammun a birnin Paris.

Mawallafi:Abdourahamane Hassane
Edita : Abdullahi Tanko Balla