1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Faɗa tsakanin 'yan taliban da sojojin Afganistan

May 8, 2011

Dakarun gwamnatin Afganistan bisa tallafin ƙungiyar tsaro ta NATO na fito na fito tsakanin su da ´yan taliban bayan jerin hare-haren ƙunar baƙin wake da aka ƙaddamar a birnin Kandhar.

Tankokin sojojin Afghanistan da ke samun goyon bayan NATOHoto: Picture alliance/dpa

Dakarun gwamnatin Afghanistan na ci gaba da fafatawa kwana na biyu a jere da 'yan taliban a birnin kandahar, bayan ƙaddamar da hare-haren ta'addaci akan gine ginen gwamnati da masu tsananin kishin addinin suka yi. Jami'an ma'aikatar cikin gidan sun bayyana cewa 'yan takifen sun yi amfani da rokoki domin aiwatar da wasu jerin hare-haren da suka halaka mutane uku, tare da jikata wasu karin 40.

Mazauna birnin Kandahar suka ce suna ji ƙarar aman bindigogi masu jigida da kuma tashin bama-bamai tun bayan da sojojin Nato suka fara mara wa dakarun gwamnati baya. Hukumar leƙen asiri na Afghanistan ta ce wannan fito na fito na daga cikin tsarin da ta tanada na sa ƙafar wando guda da taliban.

Mawallafi: Mouhamadou Awal
Edita: Yahouza Sadissou Madobi