Faɗar ƙabilanci ya bazu a Sudan ta kudu
January 3, 2012Rahottani daga Sudan ta kudu na cewa dubun-dubatan jama'a na ta ficewa domin gujewa rikicin ƙabilanci da ya ɓarke a wasu ƙauyuka dake yankin na sabuwar ƙasar Sudan ta kudu. Majiyoyi daga Majalisar Ɗinkin Duniya sun ce 'yan bindiga kimanin 6,000 daga kabilar Lau Nuer suka afkawa garin Pibor sakamakon ɗauki ba daɗi da 'yan ƙabilar Murle. Majalisar Ɗinkin Duniyar ta kiyasta cewa an kashe mutane 1,000 tun bayan da rikicin ya ɓarke. Ƙungiyar agajin likitoci ta Medicins Sans Frontieres ta dakatar da ayyuka a yankin bayan da mayaƙan suka lalata wasu asibitocinta biyu a sakamakon faɗan. An ruwaito cewa gwamnatin kudancin Sudan ɗin da Majalisar Ɗinkin Duniya na shirin tura ƙarin jami'an tsaro domin samar da zaman lafiya a yankin.
Mawallafi: Abdullahi Tanko Bala
Edita: Usman Shehu Usman