1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

faɗuwar jirgin sama a ƙasar Pakistan

April 20, 2012

Jirgin da ya faɗi a kusa da Islamabad babban birnin Pakistan ya ƙone kurmus. Babu wanda aka tsamo a raye daga cikin direbobi da fasinjoji 130 da ke cikin jirgin.

Bei einem Flugzeugunglück in Taiwan sind 79 Menschen ums Leben gekommen. Die Boeing 747 der Singapore Airlines stürzte bei schlechtem Wetter direkt nach dem Start in Taipeh ab.
wani jirgi da ya taɓa faduwaHoto: AP

A ƙasar Pakistan, wani jirgin sama da ke ɗauke da fasinjoji 130 ya faɗi a kusa da Islamabad babban birni a yammaci juma'a sakamakon rashin kyaun yanayi da ya fiskanta. Wani babban jami'an 'yan sanda na wannan ƙasa ta Asiya ya nunar da cewar jirgin ya ƙone ƙurmus, Kana ba wanda aka tsamo da ransa ya zuwa yanzu.

Wannan dai ba shi ne karon farko da Pakistan ke fiskantar haɗarin jirgin sama a shekarun baya-bayannan ba. Ko da a watan julin 2010, sai da wani Airbus ya faɗi a tsaunukan Margalla tare da salwantar da rayukan mutane kimanin 152.

Mawallafi: Mouhamadou Awal
Edita: Zainab Mohammed Abubakar