1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Facebook ya ci riba ta musamman

October 26, 2021

Facebook ya sanar da samun riba a watanni ukun da suka gabata. Alkaluman da kamfanin ya fitar a ranar Litinin sun ce kamfanin ya samu ribar sama da biliyan 9 na Dala kwatankwacin sama da Naira tiriliyan dubu dari uku.

USA Facebook Logo
Hoto: JB Le Quere/Maxppp/picture alliance

Sai dai kuma ribar ta Facebook din na zuwa ne a yayin da wata mai kwarmata bayanai Frances Haugen ta fitar da munanan zarge-zarge a game da ayyukan na kamfanin.


Tsohuwar ma'aikaciyar Faceboook din ta zargi kamfanin da fifita ribar da zai samu fiye da mutuncin kwastomominsa. Sabbin takardun da ta fitar sun ce Facebook ya kawar da kai a yayin da ake safarar mutane ta shafinsa ba tare da ya dauki mataki ba. Kazalika gwamnatin kasar Vietnam ta ba shi kwangilar dakile rubutun masu sukarta a shafinsa.


Sai dai Shugaban Facebook Mark Zuckerberg ya ce duk da cewa suna maraba da sukar da za ta taimaka musu inganta ayyukansu amma ya gamsu a kan cewa wasu na son ''gadara'' da mallakar takardun kwarmata bayanai wurin gogawa kamfanin kashin kaji.