Isra'ila: 'Yan sanda sun kai sumame a Al-Aqasa
April 5, 2023Talla
Fadan da aka yi a kan gwagwarmayar da aka dade ana yi ta mallakar masalacin na birnin Kudus tsakanin Falasdinu da Israi'la ya faru ne a daidai lokacin da Musulmi suke tsakiyar yin azumi na watan Ramadan,yayin da Yahudawan ke shirin gudanar da bukukuwan ista. Kasar Jordan da ke kula da wuraren tsarki na Musulmi a birnin Kudus, ta yi Allah-wadai da harin da aka kai a masallacin tare da yin kira ga sojojin Isra'ila da su gaggauta janyewa, yayin da Saudiyya ta yi watsi da matakin da ta ce ya sabawa ka'idojin kasa da kasa na jibge yan sanda a cikin wurin ibadar: