Ana ba ta kashi a kan iyakar Isra'ila da Gaza
May 14, 2018Talla
A wata sanarwa da rundunar sojojin Isra'ila ta fitar na cewa sojojin sun bude wuta kan masu boren a wani mataki na mai da martani don kare kai daga farmakin Falasdinawa masu zanga-zanagar.
Artabu tsakanin jami'an tsaron Isra'ila da Falasdinawan ya barke ne bayan wata zanga-zangar da aka kiyasta Falasdinawa dubu 35,000 ke yi a yankin Zirin Gaza, dab da lokacin da Amirka ke shirin bude sabon ofishin jakadancinta a Birnin Kudus.
A wannan Litinin Amirka ta bude sabon ofishin jakadancinta bayan wani biki a Birnin Kudus, duk da adawa da wannan matakin da kasashen duniya suka nunha.