Fada ya jawo rufe masallacin Kudus
July 27, 2018Talla
Sojojin na Isra'ila sun bayyana cewa kawo yanzu sun kama wasu Falasdinawa hudu don su amsa tambayoyi yayin da aka shiga kauyen Kauber da ke arewacin Birnin Kudus. An dai bayyana maharin da ya halaka dan Isra'ila da sunan iyalan da ya fito a matsayin Mohammed Tareq Dar Yousef me shekaru 17, wanda shi ma makocin wadanda ya kaiwa hari ya harbe shi da bindiga.
Kungiyar Hamas dai duk da cewa bata dauki alhaki na kai harin ba ta bayyana wanda ya kai shi a matsayin gwarzo da ke nuna halin da Falasdinawa suke ciki a wannan yanki. Wasu rahotanni na cewa biyo bayan fada 'yan sanda sun rufe kofar shiga masallacin Kudus.