1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Fada ya kazance a Sudan

Suleiman Babayo ATB
May 16, 2023

A Khartoum babban birnin Sudan lamura sun kara rincabewa sakamakon ci gaba da musanyen wuta tsakanin bangarorin da ke fafatawa fada a kasar inda aikin jinkai ya tabarbare.

Sudan I Birnin Khartum da yaki ya lalata
Yaki ya lalata birnin Khartum na SudanHoto: Mohamed Nureldin/REUTERS

Ana ci gaba da fafata fada da mayan makamai gami da jiragen saman yaki a birnin Khartoum fadar gwamnatin kasar Sudan tsakanin sojoji da rundanar mayar da martani, kamar yadda mazauna birnin suka tabbatar, inda aka kwashe kimanin wata guda ana tashin hankali. Kusan mutane 700 suka halaka yayin da wasu fiye da 5,500 suka jikata kuma harkokin jinkai suka tabarbare.

Kungiyoyin kula da agaji sun bayyana cewa kimanin mutane milyan tara suke rayuwa kusa sa inda ake fafata wannan fada.

Tuni babban habsan sojan kana shugaban gwamnatin wucin gadi, Janar Abdel Fattah Burhan ya saka hannu kan ayar dokar rufe asusun ajiya na banki na daukacin rundunar mayar da martanin.