Fadakar da Bebaye a Kano
August 15, 2017Talla
Babayen sun yaba ne a lokacin da marubuciyar da taimakon wasu daga cikin matasansu suke aikin tsara wasu littattafan na alamomin maganar hannu da ma'anoninsu. A bara ne wannan marubuciya Constanze Schmaling da aka fi sani Halima ‘yar Fulani a kasar Hausa ta kaddamar da littafi na uku da na hudu na harshen Bebayen, sannan a bana kuma ta zo da littafi na biyar wanda ta raba wa Bebaye a makarantunsu na yaki da jahilci da ke Kano.
Ta kuma yi alkawarin ci gaba da ba da gudummawa ta musamman.
"Za a ci gaba da irin wannan aiki da muke yi yanzu wato za a kara yin wasu littattafai. An buga guda dubu aka rarraba wa Bebaye kyauta."
Fafutukar da ake yi dai shi ne na ganin cewar Bebayen sun nakalci magana da hannu.