1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rikicin kabilanci ya ritsa da kabilu biyu a Sudan

Zainab Mohammed Abubakar
November 30, 2019

Kimanin mutane 26 ne suka rasa rayukansu a yayin da wasu 30 suka samu raunuka a fadan kabilanci a garin Rumbek da ke tsakiyar Sudan ta Kudu mai fama da rigingimu

Südsudan Malakal
Hoto: Reuters/B. Ratner

Karamin ministan yada labarun kasar Benjamin Laat, ya shaidawa manema labaru cewar tun daga ranar Alhamis rikici ya barke tsakanin kabilun Manuer da Gaak da basa ga maciji da juna.

Da yake Allah wadan cigaban rigingimu da ke da nasaba da kabilanci, ministan ya kuma yi kira ga mahukuntan Sudan ta Kudun, kasar da ke cikin wadi-na-tsaka-mai wuya, data dauki matakin karbar makamai daga hannun jama'a.