Darfur: Mutane 83 sun mutu a sabon rikici
January 18, 2021Talla
Sabbin alkaluman wadanda suka mutu a sabon rikicin kabilanci a yammacin Darfur na kasar Sudan ya kai 83, wasu 160 sun jikkata. Likitoci sun ce an samu mutuwar mata da kananan yara a rikicin. Sabon rikicin ya samu tushe ne bayan barkewar fada tsakanin mutane biyu a sansanin 'yan gudun hijira a birnin Genena, inda aka dabawa wani balarabe wuka har lahira a ranar Juma'a. Gwamnatin Sudan ta sa dokar ta baci a yankin tare da nada kwamitin bin ba'si. Tun a shekarar 2003, yankin Darfur ke fama da rikicin kabilanci.