Faduwar farashin mai za ta jefa Najeriya cikin matsala
December 27, 2018OPEC ta ce man fetur ya fadi zuwa dala hamsin a kan ganga daya ,lamarin da ya gaza da dala goma ga farashin dala 60 da aka daidaita kasafin kudin shekarar 2019 na Najeriya. Hakan na nufin sabon kalubale ga aiwatuwar da kasafin na kudi tun ma ba a je ko'ina ba. Ita dai kungiyar ta OPEC ta nunar cewar tana iya kokari domin cimma daidaiton farashin na mai don tabbatar da kasashen masu mai ba su fada cikin rikici ba.
Tun daga lokacin da Donald Trump shugaban Amirka ya hau mulki, ya samu hadin kan kasar Saudi Arabiyya tare da shiga rigima da kasar Iran, lamarin da ya sa harkar OPEC ta rikice. Yanzu ma haka kasar Qatar na kokarin ficewa daga tsarin OPEC, kuma yawancin mambobinta sun daina bin umarnin kididdigar yawan man fetur da ake basu damar hakowa. Wannan al'amari na da nasaba da halayyar wasu kasashe da suke da mai amma ba sa cikin kungiyar.
Evelyn Brightda ke zaman ma'aikaciyar gidan Rediyo na Jahar Rivers, da kuma ke sharhi kan al'amura daban-daban cewa ta yi.
"hakan na nufin za'a kara shiga matsatsi ke nan,lamarin ba zai yi kyau ba, dole ne mu tashi tsaye, mahukunta su lalubo mafita domin matasanmu da yanzu ke haifar da damu. Damuwar tada kayar baya za ta iya karuwa muddin rayuwa ta kara tsananta. "
Najeriya dai ta takwas ce a jerin kasashe masu arzikin man fetur a Duniya. Tana da karfin iya hakar gangar ta danyen mai miliyan biyu a kullum. Cinikin danyen mai da kasar ta yi na tsawon shekaru na biliyoyin daloli,ya kai ga 'yan kasar su fahimci wani abu na game da samar da ababen more rayuwa.