China: An dakatar da tashin jirage samfarin Boeing 737Ma8
March 11, 2019A cikin wata sanarwa da ma'aikatar zirga-zirgar jiragen saman kasar China ta wallafa, China ta ce ba za a sake aiki da samfarin jirgin ba face sai idan har bincike ya tabbatar da musabbabin faduwar samfarin jirgin na kasar Habasha wanda ake kira Boeing 737 Max 8 ne.
Kasar Indunusiya ita ma ta bayyana daukar irin wannan matakin na dakatar da daukacin jiragenta masu kalar samfarin har sai abinda hali ya yi.
Haka shima kamfanin Habashan na Ethiopian Airline ya katse duk wani aiki da samfarin jirgin face sai an gudanar da bincike game da faduwar jirginsa dauke da 'yan kasashen waje 149 da suka halaka.
Jami'an bincike sun bayyana samun akwatuna biyu da ke nadar bayyanan jirgin a daidai lokacin da hannayen jarin kamfanin Boeing suka fadi da kashi 12 cikin dari. wanda hakan ke a matsayin karonsa na farko, tun bayan wata mumunar faduwa a cikin Satumban shekarar 2011.