1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Faduwar jirgin yaki a kudancin Somaliya

May 28, 2013

Wani jirgi da ake kyautata zaton na Amirka ne wanda kuma ke sarrafa kansa da kansa ya fadi a kudancin Somaliya jim kadan bayan da 'yan al-Shabab su ka yi ma sa luguden wuta.

Hoto: picture-alliance/dpa

Wani jirgin da ke sarrafa kansa da kansa ya fadi a wannan talatar a kudancin kasar Somaliya, inda rundunar kasashen Afirka ke kalubalantar masu kaifin kishin addini na al-Shabab. Gwamnan wannan yanki Abdikadir Mohamed Nur ya nunar da cewar 'yan al-Shabab sun yi ruwan albarusai a kan wannan jirgi a garin Bulomarer lokaci kalilan kafin ya fadi. Su ma dai 'yayan wannan kungiya sun tabbatar da faduwar jirgin da ake kyauatata zaton cewar mallakar Amirka ne, ba tare da bayyana ko su suka kakabo shi ba ko a'a.

Wata kafar labarai ta Amirka ta nunar da cewa tun a shekarar da ta gabata ne mai'aikatar tsaro ta Pentagone ta tura da jiragen da ke sarrafa kansu da kansu zuwa kenya, domin taimaka wa yankin magance karancin abincin da suke yi fama da shi. Kungiyar ta al-Shabab da a ka fatattaka daga Mogadiscio a shekara ta 2011 ta na ci gaba da yada angizonta a wasu sassa na Somaliya duk da kalubale da ta fuskanta daga sojojin Kenya da kuma na Ethiofiya.

Mawallafi: Mouhamadou Awal Balarabe
Edita: Yahouza Sadissou Madobi