1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Fafaroma a yankin gabas ta tsakiya.

May 13, 2009

Ziyarar Fafaroma Benedict a yankin Palastinawa

Fafaroma a BethlehemHoto: AP


A ci gaba ziyarar da yake yi da nufin ƙarƙafa matakin tuntubar juna tsakanin mabiya addinai daban daban a yankin gabas ta tsakiya, Fafaroma Benedict na goma sha shidda ya yi kira ga samar da 'yan tacciyar ƙasa ga Falasdinawa.

A wannan larabar ce Fafaroma Benedict na goma sha shidda, ya buƙaci samar da 'yan tacciyar ƙasa ta Falastinu, kana ya bukaci matasa da su yi watsi da duk wani aikin tada zaune tsaye, game da yin kira ga kawo ƙarshen takunkumin da Isra'ila ta sanyawa yankin Gaza na Falasdinawa.

A lokacin da ya tattauna da shugaba Mahmud Abbas na Falasdinu, Fafaroma ya jaddada cikakken goyon bayan sa ga fafutukar da suke yi:

Mahmoud Abbas da FafaromaHoto: AP

" Ya shugaba! Ina nuna goyon baya na ga 'yancin al'ummarka na ƙoƙarin samar da 'yantacciyar ƙasar Falasdinu, a yankin da kuka gada kaka da kakanni, wadda zata kasance mai tsaro da zaman lafiya tare da makwabta, daidai da iyakokin da al'ummar ƙasa da kasa ta amince.

Wannan ziyarar dai ita ce ta farkon da Fafaroma ke yi a yankin gabar tekun Jordan, wanda Isra'ila ke ci gaba mamayarsa tun kimanin shekaru arba'in da biyu kenan, kana ya furta kalaman ne bayan da ya bi wani shingen da Isra'ila ta gina, wanda ya zagaye wasu yankunan garin Bait lahm, wanda kuma ya janyo cece kuce, amma Isra'ila ta ce yana da muhimmancin gaske ga tsaron ta.

Fafaroma Benedict, wanda dan shekaru tamanin da biyu a duniya, ya bukaci matasa da kar su kyale bakin rasuwar 'yan Uwa da abokan arziki, game da abubuwan da aka lalata musu ya sanya su neman daukar fansa, tare kuma da nuna juyayin sa ga mutanen da aka kashe a lokacin yakin da Isra'ila ta ƙaddamar a zirin gaza:

" Sako na ga waɗanda suka rasa iyalai da masoyansu a hare haren da aka kaddamar, musamman a tashin hankalin baya bayannan da aka yi a zirin gaza, ina basu tabbacin nuna juyayi game da sanya-su cikin addu'a a kowane lokaci.

Tunda farko, a lokacin da yake yin marhabin lale ga Fafaromar, shugaba Mahmud Abbas na Falasdinu, ya yi Allah wadai ga mamayar shekaru arba'in da biyun da Isra'ila ke yi a yankin, da kuma munanan takunkumin da ta sanya akan zirgar zirgar da ya jefa al'ummar yankin cikin wahala. Yana mai cewar akwai wasu mutanen da babu abinda suka sanya a gaba, illa kawai ci gaba da rarraba kawunan jama'a maimakon hada su, kana da tilastawa musulmi da kiristoci barin yankunansu.

Fafaroma Benedict a yammacin JordanHoto: AP

Wata mata 'yar shekaru talatin da takwas a duniya, mai suna Nevinne, wadda ke cikin kiristoci ɗari dayan da Isra'ila ta kyale su je yankin Gaza, domin ziyarar, ta bayyana ceaar jawabin Fafaromar ya ƙarfafa mata gwiwa wajen tunanin cewar, watan wata rana za'a sami tsaro da zaman lafiya a yankin.

An dai kyautata matakan tsaro domin tabbatar da nasarar ziyarar farkon da shugaban mabiya ɗarikar Katolika kimanin miliyan dubu daya da miliyan dari daya a duniya, ya kai a Isra'ila da Falasdinu, inda daruruwan jami'an tsaro ke tsaye akan tituna.

Fafsaroma Benedict zai gana da shugaba Abbas, bayan ya ziyarci sansanin 'yan gudun hijra na Aida, wanda ke wajen Beit Lah, inda 'yan gudun hijra dubu hudu da dari shidda ke zaune.


Mawallafi: Saleh Umar Saleh


Zainab Mohammed