1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Fafaroma Leo na 14 ya isa kasar Aljeriya

April 13, 2026

Fafaroma Leo na 14 ya isa kasar Aljeriya, a wata muhimmiyar ziyara irin ta ta farko da wani Fafaroma ke kaiwa kasar mai rinjayen Musulmi.

Fafaroma Leo na 14
Fafaroma Leo na 14 Hoto: Guglielmo Mangiapane/REUTERS

Ziyarar na cikin rangadin kasashe hudu na nahiyar Afirka, kuma ana sa ran za ta dauki kwanaki biyu a Aljeriya, inda zai ziyarci muhimman wuraren ibada da suka hada da babban Masallacin Algiers da kuma mujami'ar Notre-Dame d'Afrique.

A jawabin da ya gabatar bayan isowarsa, Fafaroman ya soki take dokokin kasa da kasa tare da abin da ya kira halayen "mulkin mallaka na zamani”, yana mai cewa hakan na kara janyo tabarbarewar zaman lafiya a duniya.

Ya kuma bukaci shugabanni su gina al'ummarsu  bisa adalci da hadin kai, yana mai jaddada cewa hakan ya zama dole a wannan lokaci da ake fama da rikice-rikice.

Ziyarar na zuwa ne bayan suka da ya fuskanta daga shugaban Amurka Donald Trump, yayin da ake sa ran sakon zaman lafiya zai kasance jigon tafiyarsa.