Fafaroma ya isa kasar Angola
April 18, 2026
Tun farko kafin zuwansa Angola a Yaounde da Bamenda jagoran darikar Katolika ya samu muhimmiyar tarba daga dubban al'ummar Douala kusan 120.000, Douala da yi fama da rikicin siyasa biyo bayan zaben shugaban kasa na 12 ga watan Oktoba 2025.
Fafaroman kamar a sauran wuraren da ya da taronibada ya yi kira da zaman lafiya da hadin kai domin da hadin kai ne za a iya cimma burin gina kasa da kawo zaman lafiya.
Kasancewar Fafaroma Leon a Douala na da mutukar muhimmanci inji shugaban mabiya darikar Katolika a Douala Samuel Kleda ya fadi hakan ne yayin jawabinsa a gaban dubban mabiya cocin .
Matasa da dama a Douala na zaman kashe wando babu aikin yi duk da cewa Douala ne cibiyar kasuwancin Kamaru ga tashar hawa da saukar jiragen sama ga kuma tashar jirgin ruwa inda ake hada-hadar kasuwanci shiyasa da dama daga cikinsu ke zabar mummunar hanya kamar zama yan daba masu fashi da makamai ko zuwa kasashen waje da duk hadarin dake tafe.