SiyasaGabas ta Tsakiya
Fafaroma Leo ya nemi Isra'ila ta dakatar da yakinta a Gaza
August 28, 2025
Talla
Jagoran darikar Katolika na duniya Fafaroma Leo na 14, ya yi kira ga Isra'ila da ta kawo karshen matakin da take dauka na yin hukuncin kan-mai-uwa-da-wabi a kan Falasdinawan Gaza, da tilasta musu barin muhallansu.
Fafaroma Leo ya roki Isra'ila ta gaggauta tsagaita wuta ta dindindin, sannan ta janye shirinta na mamaye Gaza baki-daya da ta sanya a gaba.
Karin bayani:Fafaroma Leo na Katolika ya ce a yi wa Gaza da Ukraine azumi
Jagoran addinin ya yi wannan jawabi ne ranar Laraba a fadarsa ta Vatican, inda dubban mabiya suka yi masa tafi da jinjina kan wannan muradi na sa, har ma ya yi kira ga Hamas da ta sako fursunonin yaki na Isra'ila da take garkuwa da su.