SiyasaTurai
Fafaroma ya bukaci masu arziki su taimaki talakawan duniya
March 28, 2026
Talla
Jagoran kiristoci mabiya darikar katolika na duniya Fafaroma Leo na shida, ya koka kan karin gibin da ke ci gaba da wanzuwa tsakanin masu arziki da matalauta a duniya, inda ya bukaci mawadata su taimaki mabukata.
Fafaroma Leo ya bayyana hakan ne a cikin jawabin da ya gabatar, a yayin ziyarar da ya kai Monaco ranar Asabar, daga birnin Rome, inda ya ce wannan tazara tsakanin masu abin hannu da marasa galihu, shi ke kara jefa duniya cikin tashe-tashen hankulan da ake gani yanzu.
karin bayani: Fadar Vatican ta yi watsi da shirin Trump
Jagoran addinin ya samu kyakkyawar tarba daga basaraken Monaco Yarima Albert da mai dakinsa Gimbiya Charlene, a wurin shakatawa na Monte Carlo.