1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaTurai

Fafaroma ya ce wajibi ne a ceci rayuka

Zainab Mohammed Abubakar
September 22, 2023

Fafaroma ya yi kira da a ceto mutanen da ke cikin hadari a kan hanyarsu ta neman tudun-mun-tsira daga wahalhalun da kasashensu ke ciki.

Fafaroma FrancisHoto: Alessandro di Meo/AFP/Getty Images

FafaromaFrancis ya bukaci da a ceto mutanen da ke cikin hadarin nutsewa yayin da aka watsar da su a kan igiyar ruwa a teku. Yayi wannan kira ne a lokacin da yake tsokaci kan yanayin tashin jijiyar wuya da ake ciki a Turai, saboda karuwar bakin haure da ke neman isa Turan ta teku daga yankunan Gabas ta Tsakiya da Arewacin Afirka.

A cikin jawabinsa da aka sadaukar ga bakin haure da suka rasa rayukansu a teku, a yayin wata ziyara da ya kai birnin Marseille na kasar Faransa, jagoran darikar roman katolika ya ce hakki ne na bil'adama kuma wajibi ne a ceci rayukan mutanen da ke cikin wahala, ya na mai gargadin gwamnatoci kan abun da ya kira "tsattsauran ra'ayi na halin ko-in-kula da fargaba mara tushe".