Fafaroma ya yi tur da ayyukan 'yan ta'adda a yankin Sahel
May 10, 2026
Jagoran kirsitoci mabiya darikar katolika na duniya Fafaroma Leo na 14, ya yi allawadai da hare-haren da aka kai kasashen yankin Sahel, musamman na Mali da Chadi kwanan nan, wanda 'yan ta'adda masu ikirarin jihadi suka kashe jama'a da dama.
Karin bayani: Mali ta ce ba za ta tattauna da kungiyoyin ta'adda ba
Fafaroma Leo ya yi wannan jawabi ne, yayin addu'o'in da ya jagoranta yau Lahadi a dandalin St Peter's na fadarsa ta Vatican, inda ya mika sakon ta'aziyyarsa ga iyalan mamatan, tare da fatan ganin karshen wannan masifa, domin samun dawwamammen zaman lafiya da ci gaban rayuwar jama'a.
Karin bayani:An sanya dokar ta baci a Tafkin Chadi
Ko a ranar Asabar an samu rahoton kisan da kungiyar JNIM, mai alaka da Al-Qaeda ta yi wa mutane 30, a kasar Mali ranar Laraba, bayan far wa kauyukansu.
Karin bayani: Fafaroma Leo ya yi kiran a yi adalci a nahiyar Afirka
Yayin da a Chadi ma 'yan Boko Haram suka halaka sojoji 26, har ma gwamnatin mulkin sojin kasar ta ayyana dokar ta-baci, ta tsawon kwanaki 20, tare da rufe iyakokinta, a kokarinta na yi wa 'yan ta'addar kofar rago.