1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Fafaroma: Za a maganta lalata da yara

March 29, 2019

Shugaban darikar Katholika na duniya, Paparoma Francis, ya bayar da wasu sabbin umurni kan yadda za a kare dabi'ar nan ta lalata da kananan yara da wasu limaman Katholikan ke yi.

Vatikan-Missbrauchskonferenz Papst Franziskus
Hoto: REUTERS

Umurnin wadanda suka shafi malaman darikar na yankin Vatikan, na zuwa ne bayan wani taron koli da jagororin darikar suka yi kan matsalar cikin watan jiya.

Cikin sanarwar da fafaroman ya fitar, akwai dokokin da suka dora alhaki kan jami'an fadar ta Vatikan su sanar da duk wani da ake zargi da lalata da yara.

Haka ma fadar Fafaroma, ta bayyana yiwuwar nada wani jami'i da za a rika tuntuba kai tsaye cikin fadar a kan duk wani abin da ya shafi wannan laifi.