Fafatawa da masu zanga-zanga a Hong Kong
September 28, 2014Talla
Al'ammura sun tsaya cik a birnin, inda a wannan Lahadin jami'yan tsaro na 'yan sanda sukayi amfani da hayaki mai sa hawaye, ga dubunnan masu zanga-zangar neman girka Dimokradiya, da suka ce babu gudu ba ja da baya a kokowar da suke, wajan ganin sun samu karin walwala ta siyasa, daga hukumomin Chine.
Masu zanga-zangar dai sun cika wata mahimmiyar hanya ce dake tsakiyar birnin, abun da ya haddasa matsalolin zirga-zirga, inda jami'yan tsaron na 'yan sanda sukayi amfani da hayaki mai sa kwalla don tarwatsa masu zanga-zangar yanayin da ba'a cika samun sa ba a Hong Kong.
Mawallafi: Salissou Boukari
Edita : Umaru Aliyu