1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Labarin Wasanni: Fafatawar karshen mako

Abdulkarim Muhammad Abdulkarim
October 19, 2026

Hukumar Kula da Wasannin Guje-guje da Tsalle-tsalle ta Duniya ta bayyana gasar Nairobi babban birnin kasar Kenya ta 2029, a matsayin gagarumar dama ga Afirka ta tallata kyawawan manufofinta ga duniya.

Wasanni | Kenya | Sebastian Coe
Shugaban Hukumar Kula da Wasannin Guje-guje da Tsalle-tsalle ta Duniya Sebastian CoeHoto: Ronald Zak/AP Photo/picture alliance

Hukumar Kula da Wasannin Guje-guje da Tsalle-tsalle ta Duniya WA ta ce, gasar da za a gudanar a birnin Nairobi fadar gwamnatin kasar Kenya a shekarar 2029 za ta zama ta musamman kuma nagartacciya da za ta tallata manufofi da tsare-tsaren nahiyar Afirka ga duniya. Hukumar ta bayyana hakan ne kasancewar ita ce gasa karo na farko da ake yi a Afirka, bayan doke fitattun biranen duniya na London da Rome a takarar neman daukar nauyi.

Shugaban hukumar Sebastian Coe ne ya nuna wannan kyakkyawan fata, lokacin da ya ke ganawa da shugaban Kenya William Ruto yayin ziyarar duba aiki da ya kai a makon da ya gabata. Ya  shawarci kasar da ta kara himma, wajen aiwatar da ayyuka ingantattu a shirye-shiryen daukar nauyin gasar. Ya ce dama ce gagaruma ta tallata kanta a duniya, la'akari da yadda za ta karbi bakuncin gasar cin kofin kwallon kafar nahiyar Afirka a 2027 da hadin gwiwar makwabtanta Tanzaniya da Yuganda.

Dan wasan damben Birtaniya Daniel Dubois a fafatawarsa da Oleksandr Usyk Hoto: Andrew Couldridge/Action Images/REUTERS

Fitaccen dan wasan Birtaniya Daniel Dubois ya kare kambunsa na WBO ajin masu nauyi bayan nuna bajintar da ya yi a wajen ragargazar takwaransa na Birtaniya Fabio Wardley a zagaye biyu kacal, wato mintuna biyu da dakika 21 na fafatawar da ta gudana a dandalin O2 Arena na birnin London cikin daren Asabar. Karawar ta dara wadda gwarazan biyu suka buga a cikin watan Mayun da ya gabata, wadda ita ma Dubois din ya samu nasara.

Wannan nasara ta kara daga likkafar Dubois mai shekaru 29, sakamakon kara haskakawar tauraruwarsa da ke shirin fara sajewa da manyan kwararrun damben duniya. Ya samu nasarar a lokacin da zakakuran fagen wato Tyson Fury da Anthony Joshua ke shirin tunkarar juna a watan Disambar 2026, kuma wanda ya yi zarra a cikin wadannan 'yan Birtaniya ka iya karawa da Dubois a nan gaba. Hakan kuma, zai kara daga darajarsa a duniya.

Likkafar Sonay Kartal ta Birtaniya ta yi gabaHoto: picture-alliance/P. Royer

Likkafar 'yar wasan Tennis ta Birtaniya Sonay Kartal ta yi gaba bayan da aka ayyana ta a matsayin lamba daya a kasarta, duk kuwa da rashin nasarar da ta yi a hannun 'yar wasan Poland Maja Chwalinska a wasan karshe na gasar Wuhan Open. Kartal ta sha kashi da ci 2-6 6-4 6-2 a garin Wuhan na lardin Hubei a kasar China, bayan gumurzu a ranar Lahadi.

A jadawalin da Hukumar Kula da Kwallon Tennis ta Duniya WTA ta fitar ya nuna cewa, Chwalinska ta Poland ta haye zuwa matsayi na 11 daga mataki na 22 da ta ke kai a baya. Yayin da ita ma Kartal ta Birtaniya ta samu karin matsayi zuwa na 49 a duniya, maimakon mataki na 170 da ta ke kai a daidai lokacin fara gasar Wuhan Open.

 

Tsallake zuwa bangare na gaba Bincika karin bayani