1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Birnin Hasakeh ya zamo filin daga a Siriya

Lateefa Mustapha Ja'afarJune 5, 2015

Ana ci gaba da gwabza kazamin fada tsakanin dakarun gwamnatin Siriya da mayakan kungiyar ta'addan IS a birinin Hasakeh na arewa maso gabashin Siriya.

Tashin hankalin da kasar Siriya ke fuskanta
Tashin hankalin da kasar Siriya ke fuskantaHoto: REUTERS/B. Khabieh

Bangarorin biyu dai na wannan dauki a ba dadi ne a kokarin kwace iko da birnin Hasakeh da ya kasance babbar gunduma da ke da matukar muhimmanci a yankin arewa maso gabashin kasar ta Siriya. Kungiyar kare hakkin dan Adam da ke sanya idanu a yakin na Siriya ta sanar da cewa dakarun gwamnatin Siriyan na barin bama-bamai a kan maboyar 'yan ta'addan na IS da ke birnin. Tun dai a ranar 30 ga watan Mayun da ya gabata ne aka fara wannan bata kashi tsakanin dakarun na Siriya da mayakan IS din, inda mayakan na IS suka matsa kaimi wajen kai hare-haren kunar bakin wake a kudancin birnin na Hasakeh a kokarin da suke na kwace iko da garin da ya raba yankunan da ke hannun gwamnati da kuma wanda ke hannun Kurdawan kasar Siriyan.