1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kokarin samar da shugabanci a Sudan ta Kudu

May 2, 2019

A birnin Addis Ababa na Habasha bangarorin da basa jituwa a shugabancin kasar Sudan ta Kudu suka zauna a teburi guda da za su shafe kwanaki biyu suna tattaunawa, don sulhuntawa da juna ta hanyar kafa gwamnatin hadaka.

Südsudan Präsident Salva Kiir und Vizepräsident Riek Machar
Hoto: picture-alliance/dpa/P. Dhil

Tun a cikin watan Satumbar bara ne dai Shugaban Sudan ta Kudu Salva Kiir da jagoran tsagin masu tawaye Riek Machar gami da wasu tsirarun jiga-jigan 'yan adawa suka rattaba hannu kan wata yarjejeniyar zaman lafiya, to sai dai tun kan a kai ga cin Talata da Laraba bangarorin suka gaza cimma yarjejeniyar rabon madafun ikon da ake fatan ya tabbata a ranar 12 ga watan Mayun nan da mu ke ciki.

Kungiyar nan mai rajin ciyar da yankin gabashin Afirka gaba ta IGAD ce dai ta jagoranci zaman na Alhamis din nan, wanda gwamnatin Sudan ta Kudun ke fatan za a a kai ga cimma matsaya cikin lumana, to amma tsagin Riek Machar na da muradin ganin an jinkirta wannan matsaya da karin watanni shida nan gaba, don ganin an cimma warware wasu matsalolin tsaro da ma wasu al'amuran da suka yi wa Mista Machar tarnakin koma wa kasar, inda ya so sai an kai ga batun kafa gwamnatin hadakar.

MDD na kokari wajen ganin an zauna lafiya a Sudan ta KuduHoto: picture alliance/AP Photo/J. Patinkin

Puot Kang Chol jigo ne a bangaren 'yan adawa kuma guda cikin wadanda suka halarci zaman sasantawar na birnin Addis Ababa, ya ce fatansu shi ne a kai ga cimma dunkulalliyar matsaya da za ta kai kasar Sudan ta Kudu ga tudun mun tsira, amma ba wani lamari na radin kai ba.

Wannan zama dai ya gudana tare da sa idon wakilai daga bangaren Majalisar Dinkin Duniya, inda Mista David Shearer ne jagoran tawagar ta Majalisar Dinkin Duniya tun a shekarar 2016, ya ce dukkan bangarorin biyu suna ba da hadin kai kamar yadda ake bukata wajen cimma sulhu.

Tun bayan samun 'yancin ne dai a 2011 rikici ya barke wanda ya yi sanadiyyar mutuwar mutane akalla dubu dari uku da tamanin, tare da tilasta mutane fiye da miliyan hudu yin gudun hijira, wanda kuma daidai yake da kaso daya bisa uku na al'ummar kasar. 

 

 

 

Tsallake zuwa bangare na gaba Bincika karin bayani