Fafutukar yaki da ta'addanci a yankin Sahel
December 13, 2017![Macron und Merkel beraten mit Sahel-Ländern](https://static.dw.com/image/41785814_800.webp)
Talla
A taron da aka gudanar a kusa da birnin Paris, shugaban Faransa Emmanuel Macron ya ce dole ne, su samu nasara a yakin da 'yan ta'adda a yankin Sahel. Shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel da firaministan Italiya Paolo Gentiloni na daga cikin wadanda suka halartarci taron.