1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ina makomar siyasar Biya a yankin arewacin Kamaru?

Zakari Sadou ZMA
June 30, 2025

Ra'ayoyi sun banbanta a Kamaru kan matakin Bello Bouba Maigari da Issa Tchiroma Bakary na tsayawa takarar zaben shugaban kasa.

Hoto: Wu Hao/AP Photo/picture alliance

A karshen makon da ya gabata ne Issa Tchiroma Bakary da Bello Bouba Maigari suka yanke kauna da Paul Biya suka rungumi kaddara suka sanar da shiga zaben shugaban kasa na 2025.Wannan matakin shiga zaben shugaban kasa, ya janyo bacin rai ga 'yan jam'iyya mai mulkin kasar, wasu kuma na cewa sun yi daidai da suka raba kafa da Paul Biya duk da kuwa ana iya daura musu laifin lalacewar kasar a matsayinsu na jam'iyyun kawance.

A cewar masanin tattalin arziki Dieudonné Essomba, Bello Bouba da Issa Tchiroma sun lura cewa Kamaru ta zama tamkar mota marasa matuki shi yasa suka janye.

"Bello Bouba da Issa Tchiroma sun yanke shawara goyon bayan mutumin da ake gani, mutumin da yake daukan nauyin ayyukan da ya yi, wanda za su iya ganawa, sai kuma ya zama cewa wannan mutumin sakamakon rashin lafiya da kuma yawan shekaru, ya janye ba a ganinsa sai dai wasu mutane ne ke gudanar da ayyuka a madadinsa, za ku yarda mutane masu hankali su ci gaba da aiki a irin wannan yanayi"?

Hoto: Wu Hao//Pool EPA/AP/dpa/picture alliance

Bello Bouba Maigari mai shekaru 80, yayin da Issa Tchiroma Bakary ke da shekaru 78, wadannan gogaggun yan siyasa sun kama mukaman ministocin Paul Biya sau da dama.

Yayin da wasu ke kallon raba gari da Paul Biya a wannan lokaci na zaben shugaban kasa ka iya kassara karfin jam'iyya mai mulkin kasar. Sai dai Fadimatou Minche Bengono 'yar siyasa mai goyon bayan takarar Paul Biya a zabe mai zuwa ta shaida wa DW cewa, wannan abin da ya faru ba zai hana jam'iyya mai mulki ci gaba da mamayar arewacin Kamaru ba.

"Mu a RDPC a bin da yake gabanmu shi ne ci gaba da aiki, saboda muna sauraron abubuwa da mutane ke cewa a shafukan sada zumunta "RDPC ta mutu karshenta kenan a arewaci" ina so ku sani duk girman arewacin Kamaru na da gundumomi 84, idan kuka duba karshen zabukan da aka yi, UNDP na da kananan hukumomi 16 ko 17, MDR na da uku, FSNC na da uku, sai kayi lissafi cikin 80 nawa zai saura na RDPC''

Wannan na nuna cewa kawo yanzu jam'iyya mai mulki ta fi rinjaye a fadin arewaci, sai dai dakatar da kawance da jam'iyyun adawa biyu suka yi ka iya tarwatsa jam'iyya mai mulki domin labari na yaduwa cewa, nan da 'yan kwanaki masu zuwa jam'iyyar za ta fuskanci sauya sheka zuwa UNDP da FSNC saboda dakatar da kawance da suka yi da Paul Biya. Amma wannan ba shi ne tabbas za su iya samun mafi yawan kuri'u daga al'ummar arewacin kasar ba, saboda kashin kaji da RDPC ta shafa musu sakamakon tsawon lokaci da suka kwashe suna aiki tare ba sa iya wanke kansu da zarge-zarge da hannu a lalata kasar ba, inji Farfesa Eric Mathias Owona Nguini masanin harkokin siyasa

Hoto: Henri Fotso/DW

"Ba za su iya ware kansu a matsayin wadanda suka yi kawance tsawon lokaci da wannan gwamnati ba, wannan na nuna tsohuwar dabarar 'yan siyasa wacce ta yi zamani tun shekarar 1950, ga makomar demokuradiyar Kamaru mummunar alama ce".

Rashin hadin kan 'yan adawa a Kamaru domin tunkarar zaben shugaban kasa na watan Oktoba ka iya bai wa RDPC damar ci gaba da mulki har sai abin da hali yayi ko da kuwa Paul Biya bai sanar da takararsa a wannan zabe ba.