Fagen siyasar Ukraine bai sauya ba ko bayan zaben raba gardama
May 15, 2014![Ukraine Konflikt Pro Russland](https://static.dw.com/image/17589510_800.webp)
Talla
Har yanzu dai tsugunne ba ta kare ba a Ukraine, inda ko bayan da suka gudanar da zaben raba gardama suka bayyana anniyarsu ta gamewa da Rasha 'Yan a-waren yankin gabashin Ukraine na cigaba da janyo tashe-tashen hankula a kasar musamman wajen arrangaman da suke yi da jamian tsaro.